Kalaman Soyayya

Kunsa Yanda ake furta kalaman Soyayya ? Nasan Am’sar itace…. ku garzayo kuji kalmar so daga bakin masoyan asali

Zuciyarki ta zama takarda, tawa ta zama biro in rubata miki shafin kauna ! Kizama kofa na zamao makulli, mu hadu mu bude kofar soyayyar lambun zuciyata!

Kunsa Yanda ake furta kalaman Soyayya? Nasan Am’sar itace….

ku garzayo kuji KALMAR SO daga bakin MASOYAN ASALI

Kutabbatar Kunyi like kafin ku fara karantawa…. Dan samun Wani
https://www.facebook.com/taskarso

Zuciyarki ta zama takarda, tawa ta zama biro in rubata miki shafin kauna !

Kizama kofa na zamao makulli, mu hadu mu bude kofar soyayyar lambun zuciyata!

Na kasa tsaye na kasa zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro , kin fita daban kaman wata a daren sha biyar!

Ya madarar zuciyata, ki zamo ciminti in zamo bulo mu gina gidan quana a filin soyayya.

Watau yau da na tashi, sai na ga rana ta taso ta haske garin nan, amma duk hasken ta ba kai hasken fuskar da haske zuciyata,

domin ni a zuciyata Hasken fuskar abun quana ta yafi duk hasken raina

Ki zama petur na zama inji mu hadu mu taa da lantarkin qauna
ya shiba ta na baki filin zuciya ta

ki shuka a duk wani lungun da sako bushiyar so a kaunadon mu sami inuwar da zamu zauna muyi soyayya.

Kece madubi abar dubawata duk safiya,

kin zamo min tamkar fetur a mota,

rayuwat ba kelami ce ya rabin raina.

Ke ce makwarariyar madarar zuciyata, wadda da na sha za ta haska ka zuciyata ta yi fari.
.
Rayuwata babu ke tamkar wayar da ba wayarshaji ce, kuma babu layi, a mace ba amfani.

Kunne ya kurmance saboda rashin jin kallamen quanar ki kullum,
baki ya daina magana dai dai saboda rashin begen zumar rayuwata kullum.

Ta tsagwaron zallar tsabar kwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda rashin ganinki a yau da kullum Ya gangariyar madarar zumar da bata da gauraye,

ya tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske zuciyar masoyinta.

Idona ya bude ya ga haske irin na walkiya don ya gan ki.

Ziciyata na shan lawgadar zuma da madarar kauna Idon basira lafazin rayuwata Alfijir na quana ya keto,

tsuntsayen soyayya sun tashi su na yayo a sararin samaniyar zuciyata Ya fankar da ke juya zuciyata,

zan zamo kwalekwale ki shigo bu hau kan kogin so,

in zamo katifa ki zamo gado a cikin dakin kauna.

Hadarin begen ki ya hado, guguwar sonki ta taso, sai ruwa mai karfi ake yi na kaunar ki a filin zuciyata.

Gaisuwa daga kamfanin so, harabar kauna,

gida mai lambar zuciyata layin begen ki, zuwaga rabin rayuwata.

ya zare da allurar da ta dinken zuciya ta,

bazan taba daina sonki ba har sai wutar lantarki ta zauna a nijeriya.

ya majaujawar zuciya ta, zan zama guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu cikin rijiyar soyayya.

Ya tsokar zuciya ta, zan so ace ki zama fura in zama nono mu hadu a kwaryar soyayya.

Ya sahiba ta ki zama fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu ta da tsuntsun soyayya.

Ya masoyiyata, ki zamo bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar da ke.

Ya masoyiyata, ki zamo hanta in zamo jini, muga mai raba mu.

Ludayin kaunar ki ya mamaye min kokon zuciyata.

Ya masoyiyata, ki zamo mai in zamo alabasa mu hadu mu soye juna.’.

a masoyiyata, ki zama candir in zamo ashana, ku zamo itace in zamo makamaci mu hadu mu hura wutar so, domin mu mu tafasa tukunyar kauna.

Aminci Agareku

Barka da zuwa

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: