Budurci Na Gidan Miji Na
Daure ka/ki tura wa wani koda baza ka samu damar karantawa ba burin mu ya isa gurin iyayen mu
Assalam alaikum ‘yan uwa musulmai dan ALLAH duk wanda ya samu wannan sako yayi kokarin turawa gaba har ALLAH yasa iyayen mu suji koda labari ne agun wasu, ba na rubuta ko dan tozarta wasu iyayen bane, na rubuta ne dan abi mana hakkinmu * Budurci Na Gidan Miji Na * a nan ya kamata na sauke shi.
A gaskiya iyayen mu na yanzu basa mana adalci ko kadan, mun kasance masu son aure amman sai suce za muyi karatu kamar su sun yi, wannan shi ne babban kuskuren da ake samu, wallahi duk wanda dan shi, ko ‘yarta ta lalace ita ta ga dama da bata yi maganin matsalar tun daga farko ba, domin icce tun yana danye ake kokarin lankwasa shi kafin ya girma ya bushe.
Ana samun babban kuskuren da ku kuke sa mu, ana barin mu muna tafiya karatu ba asan me muke yi ba, ba asan me muke kallo ba, ba asan me muke yi ba, ba a san me muke ji ba, ba a san su waye malaman mu ba, balle kawayen mu!!!
Ana cutar da mu wanda hakan yasa muke samun matsaloli na kallon fina finan batsa da hotunan batsa, wanda hakan yake sawa muce zamu gwada muji dadin da ke ciki.
Wallahi iyaye kuji tsoron ALLAH ku taya mu rike mutuncin mu, amana aka baku mu kafin ranar da za ku kai mu gidan mazajen mu, kuna jawo mana zunubai, ganin mun samu duniya don muyi boko mu zamo wasu abin kwatance wanda hakan bayi bane a gurin ALLAH.
Ku rufawa kanku asiri kurufa mana muma, wallahi zaku kashe mu tun bamu san dadin aure ba, zaku mayar da mu zawarawa tun ba muyi aure ba, kuna jefa mu ga halaka, kuna cin amanar mu, aure baya hana karatu kuma dole sai da aure za a samu damar yin karatu hankali kwance, sai kuga wata a kalma sunanta budurwa amman a zahirance ba budurwar ba ce, sabida ta tsiyaye budurcin duk ya kare a hanyar makaranta.
Darajar mu gidan miji tunda har muka kawo kukan mu gurinku ku yi hakuri kuyi mana, kafin ALLAH yayi fishi da ku saboda danne hakkinmu da ku kayi.
Duk mai kishin ALLAH da manzon sa, duk mai neman rahmar ALLAH da manzon sa, duk wanda ya yarda da ayar alqur’ani ya yarda da musulunci gaskiya ne ya yarda da aure sunnar annabi (s a w) ya turawa ‘yan uwa domin sako ya isa gurin iyayenmu, su fito da mu halin da suka jefa mu, sannan su nemi yafiyar ALLAH irin halin da suka jefa mu wannan shine Budurci Na Gidan Miji Na .
ALLAH ya taya mu kare mutuncin mu kafin mu je gidajenmu (ameen)
Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa
Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.