Na rubuta Littafin ne don rayuwata ta ci gaba ko bayan na mutu: Hajiya Dadasare
A shafi na 96 na littafin Hajiya Dadasare mai suna ‘It Can Now Be Told’ ta fada cewa, “na rubuta littafin nan ne don ya rayu bayan bani nan, ‘yan baya su samu darasi, sannan in karfafa guiwar cewa mace na iya bada duk wata gudummuwar rayuwa in har ta samu dama”.
Labarin na da ban Tausayi yadda aka hada kai da ‘yan uwanta aka sace ta, aka kaita cikin wadanda baturen jami’i daga Ingila ya dauke ta ya sanya ta a daka ya mai da ta kamar matarsa har suka haifi da daya.
Da yadda ta koma wajen wani Baturen a Zaria. A nan tayi rayuwarta in da tayi aikin jinya da aikin jarida tare da Gaskiya Tafi Kwabo, aikin fadakar da Mata da koya masu sana’o’i.
Daga nan ta rika tafiya Ingila da Amurka karo ilmi don tazo ta taimaki mata a arewacin kasar nan, da shirya kungiyoyi mata don fadakar dasu.
Dadasare, bata kara haihuwa ba amma ta rika rike ‘ya ‘ya tana basu tarbiyar da yanzu zuriyar sun yi fice daga cikin su har a gidan walin Daura ta jihar Katsina.
A 1977 ta bar Zariyar ta koma garinsu, a jahar Adamawa, duk rayuwarta ta rika rubuta duk wasu muhimman abubuwa na rayuwarta a wani kundi. Wanda yanzu haka yana wajen wata malamar jami’a mai suna Dakta Aliya.
Bangaren rayuwarta na karshe yafi ban tausayi, inda ta kira diyarta mai suna Aisha Giraldo, da ke auren Walin Daura, tace “kina iya zuwa Gombe a gobe”, tace “gani nan tafe”.
Tace, “in kin zo baki iske ni ba, ki duba kasan filo na bar maki sakon wata takarda”, Aisha tace me kike nufi?” Taki bata amsa.
Da yamma ta ce wa yaronta, “daga gobe, ba zaka kara gani na ba”
Yace “hajiya me kike nufi?” taki bashi amsa.
Da asuba ta gama sallar asuba, sai kawai ta fada rijiya don ta kashe kanta da kanta, amma bata kai ga mutuwa ba, aka fito da ita, ta rasu a asibiti bayan kwana uku da fadawarta rijiya.
Ta bar duniya, ana ta tambayar me yasa tayi yunkurin kashe kanta? Alhali ba abin da ta rasa a duniya?
Tayi suna, tana da kudi, jama’arta na sonta da alfahari da ita?
Daga Taskar labarai
Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa
Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.