Sako Na Musammam
Da farko ina mika godiya mara iyaka a gareku tare da fatan Allah ya cigaba da yimana jagora a rayuwarmu gaba daya...
Ina son amfanin da wannan dama na tunasar damu abun da muka sani tun tini dangane da yanayin siyasar wannan kasa (Nigeria), a tsakankaninmu yara, matsakaita da manyan mu ta yadda mafi akasari kan nemawa kansu bangaren siyasar da suke kyautata zaton zasu samu damar gudanar da ayyukansu da cikar burukansu ba tare da samun tsaiko ba….
Kusan sati uku kenan ana tattaunawa akan yanayin siyasar da Biyora ya samu kansa a cikinta, bayan da labari ya bayyana cewa na canza sheka zuwa tsagin gidan Alhaji Atiku Abubakar, bayan sanin da akayimun a bangaren tafiyar Baba Buhari, wannan abu ya janyo maganganu masu yawa musammam ga wadanda suke zaton kamar hakan bazai taba faruwa ba, wasu kuwa har gobe sun kasa aminta da cewa zan iya rabuwa da Baba Buhari a siyasance, duk da cewa nima ina da nawa burikan da suka sanyani yanke hukuncin dana yanke…..
Komawar da nayi a tafiyar Gidan Atiku Abubakar na kusan wata daya, na samu dunbin ilmin siyasar gidan da kuma fahimtar kudirce kudircen su, hakan yasa na kara fahimtar irin burikan da yake dasu idan ya samu damar samun mulki a shekarar 2019, tabbas kyawawa ne idan har za’a iya aiwatar dasu, ina cikin tunanin tunkarar sabon aikin sanar da duniya wadancan gwala gwalan tanade tanaden dan takarar mu, sai wani mai bibiyata ta wannan kafa ya aiko min da sakon kar ta kwana wanda ya fara cewa” Malam Rabiu Biyora ka Burgeni matuka kan yanda ka zamto mutuminda bai manta Alkhairi tare da yin siyasa ba da gaba ba, ni dan uwanka ne matashine daga karamar Hukumar Nasarawa ta jahar Kano, ka burgeni matuka kan yanda ka kasa mantawa da karamcin dake tsakanin ka da Hadimin Shugaban Kasa Kan Kafafan yada labarai Mallam Shaaban Sharada, hakika wancan matashi abin alfahrine ga kafatanin matasan kano, yayyafi ne dake sauka kan masoya muhd Buhari manya da yara, Mutum ne mai hikimar wayar da kan masoya shugaban kasa, adon haka nake fatan zaka saurari sakon sautin mai dauke da Muryar wancan bawan Allah da ya gabatar a daya daga cikin gidajen radiyon da yake shirye shirye, inda yai karin haske kan nasarar da shugaban kasa ya samu da kuma fashin baki na kudurinsa a zango na 2 wato next level, na barka lafiya”..
Bayan da na saurari sautin da wancan bawan Allah ya aiko min mai dauke da muryar Shugaban Buhari sai na dogon nazari inda na kwatanta su da kudurce kudurcen Alh Atiku Abubakar nan take na fahimci akwai bukatar in sake komawa ga Shugaban Buhari domin cigaba da bayar da gudummawa ta a gareshi.
Duk da cewa na samu abubuwan more rayuwa kamar yanda Dan Adam ke bukata daga wajen Alh. Atiku Abubakar da masoyansa, rayuwata ta sauya na samu kulawa ta musammam irin wacce ake nema a siyasa, amma sai na kula da cewa yin abun da al’umma gaba daya zasu amfana yafi wanda ni kadai zan amfana da wasu yan kalilan, wannan dalilai suka tilastani yanke shawarar in kara komawa bangaren Baba Buhari don tabbatuwar burin da yake dashi a zabukan 2019, na inganta rayuwar talakawan dana fito daga cikinsu, shine abun daya kamata na kalla ba biyan bukata ta ni kadai ba, domin tun daga ranar da na dawo wannan tafiya na samu tarba ta kirki a babban birnin tarayya abuja, bansan matsalar sauro ba ballantana dauke wutar lantarki, abinci kullum mai rai da lafiya ga mukamukan nama acikin miya, duk abun danakeso ake yimun, wanda hakan ya nemi in fara mantawa da rayuwar mutanen dana fito daga cikinsu wato talakawa…
Tabbas ina da babban burin samun damar dazan temakawa kaina da wasu, amma samun biyan bukatar al’umma gaba daya itace kan gaba….
Cikin Girmamawa tare da yabawa Alhaji Atiku Abubakar tare da iyalansa nake bayyana komawata gidan dana fito na tafiyar Baba Buhari, tare da hakura da dukkan alheran da ni kadai ne nake samu a kyakkyawar muamular da mukeyi ni da iyalan gidan Atiku Abubakar…..
Zan cigaba da tsayawa a inda aka sanni nayin siyasa ba tare da cin zarafi ko aibatawa ba, da haka nake cewa ina bayar da hakuri ga dukkan mutanen da bazasuji dadin wannan mataki dana dauka ba, sannan nake yafewa dukkan wadanda suka aibatani ko zagina saboda canza shekar siyasa danayi a farkon wannan watan…
Zamana a Biyora mai hawa Babur mai kafa biyu shi na zaba in har shugaba Buhari zai samu damar karasa babban aikin daya dauko na inganta rayuwar talakawa yan’uwana.
Kuma kaura a siyasa bisa dalilan da yasa mutum ya shiga siyasar halak ne, Muhammadu Buhari ya shiga APP, ANPP, CPC da APC don cikiar burinsa.
Alh. Atiku Abubakar ya shiga SDP, PDP, AC, PDP, APC ya kuma koma PDP inda burinsa na zama dan takarar jam’iyyar ya cika a shekarar bara.
Rabiu Biyora ya fara da PDP, APC, PDP yau kuma na koma APC don cikar Buri na kyautata Rayuwar talaka.
Nagode Allah ya temaka mana a dukkan lamarinmu…
Ina alfari da dukkan mutanen da muke tare a wannan dandali….
You must log in to post a comment.