RayuwaSoyayya

Namiji : Salma tasaka kuka ta goge sunan danta 1 tilo

NAMIJI : Wata rana a makarantar manya malamin koyar da sanin halayyar dan Adam (Psychology), ya shiga aji yace "yau zamu yi wani wasa", "me ? wasa".

NAMIJI : Wata rana a makarantar manya malamin koyar da sanin halayyar dan Adam (Psychology), ya shiga aji yace “yau zamu yi wani wasa”, “me ? wasa”.

Malam yace a cikinku wa zai fito gaban allo a fara da Shi ?

Sai wata daliba Salma ta fito, Sai malam yace ta dauki alli (chalk) ta rubuta sunan mutane 30 masu muhimmanci a rayuwarta,Salma ta rubuta dangi, kawaye, abokan karatu da makwaftanta.

Sai malam yace ta goge 3 wadanda basu da muhimmanci sosai a wajenta, Salma ta goge suna 3 na abokan karatunta.

Sai malam yace ta kara goge 5 marasa muhimmanci, Salma ta goge makwaftanta, Malam yayi ta umartarta tana gogewa har sai da ya rage sunaye 4 ka dai sune :-

Babarta, Babanta, Mijinta da Danta 1 data haifa.

Gaba dayan dalibai sai suka nutsu sun gane cewa wannan ba wasa bane kamar yanda Malam ya fada da farko, yazo musu ne da wani darasi mai muhimmanci.

To ! Sai malam ya kalli Salma yace ta kara goge 2 daga sunayen nan da suka rage, wannan zabin fa yana da wuya, Salma tayi jimmm ! Hannunta yana rawa ba’a son ranta ba idonta ya cika da kwalla ta goge sunan Babarta da Babanta.

Sai malam yace ta kara goge 1, Sai Salma tasaka kuka ta goge sunan Danta 1 Tilo Sai malamyace ta koma wajenta ta zauna.

Bayan wani dan lokaci sai malam yayi tambaya, yace :- ” me yasa ta bar mijinta” namiji ?

Iyayefa sune suka kawo ki duniya suka raine ki har kika girma,Danki kuma ke kika yi cikinsa kika sha wahalar laulayin cikin kika haife shi, kika raine Shi, kuma da iyaye da Da bazaki iya sake wadansu ba, amma miji ko yaushe zaki iya chanja wani.

Aji akayi shiru ana jiran amsar Salma, Salma cikin nutsuwa da sanyin murya tace :-

“Wata rana iyayena ina tare dasu suka dauke ni suka kaini gidan miji, idan na kawo musu ziyara sai su tambayeni, “lafiya” ?

Idan yayi min laifi na taho gida sai su kira Shi suyi ta bashi hakuri, suce na tashi na koma gidansa”.

Da na kuma wata rana zai barni idan ya girma ya mai da hankali kan sana’arsa da hidimar iyalinsa,Mutum 1 wanda zai kare rayuwarsa tare da ni shine MIJINA , kuma…… Kafin ta kara magana sai dalibai suka dauki tafi gaba daya saboda ta fadin gaskiyar yanda rayuwa take.

Sai malam yace :- “Gaskiya ne, Allah ya sanya aure a tsakanin miji da mata ya zama dangantaka ta tsowon rayuwarsu, Ko yaushe ka girmama abokin rayuwarka (miji ko mata).

Allah ya sanya miji da mata su zama Abu 1 Kamar yanda yazo a al- qur’ani mai tsarki, Allah yana cewa :- ” yana daga cikin ayoyinsa ya halitta muku matayenku daga jikinku, don ku rayu dasu, ya sanya a tsakaninku soyayya da jin kai, hakika a cikin wannan akwai aya ga ma’abota tunani”.

Don haka ku ( ma’aurata) ku zaku saka wannan dangantaka ta zama sama da kowace dangantaka a duniyar nan Kafin mutum yayi aure Allah da manzansa sune a farko sannan dangi, bayan kayi aure Allah da manzansa suna farko miji/ mata sune na 2 Saman dangi, Ma’aurata ya zama wajibi ku baiwa aurenku abinci ya girma yayi karfi, abincin kuwa shi ne bin dokokin Allah, Gaskiya, rikon amana, Hakuri, Zaman lafiya Soyayya da Nishadi.

Namiji

FATAN ALKHAIRI GA DUK MASU AURE.

Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa

Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: