Aure
Aure,- Wani yare a Uganda ya bada damar kanwar uwar amarya ta “dandana” Angon kafin aure
– Wani yare a kasar Uganda yazo da wani salon tantance ma mace miji wanda ya bambamta da sauran yarikan Afirika
– A al’adun Afirika da, kannin uwa an sansu da bada shawarwari ne da dabarun zama da miji kafin aure
Afirika dai nahiya ce mai girma, tana da albarkatun yarika da al’adu daban daban da suka hada da Zulu, xhoha, Himba, inyamurai, hausawa da kuma yarbawa. Nahiyar tana takama da kusan yarika dubu uku. Su dai yaren Banyankole a kudu maso yammacin kasar Uganda dai abin ya bambamta. Idan masoya zasuyi aure, daya daga cikin amfanin kanwar uwa shine ta kwanta da Angon domin tantance jarumtarshi da kuma tabbatar da cewa zai iya haihuwa. Zata kuma duba amaryar domin tabbatar da budurcin ta kafin ayi auren.
A wasu al’adun ma Angon da amaryar zasu sadu a gaban kanwar uwar don tabbatar da komai na tafiya daidai. Duk da dai zamuji wannan al’ada bambarakwai amma tana nuna mana yanda mutanen Banyankole suka dau budurci da muhimmanci. Yarinya tana kai shekaru 8 da haihuwa ake sanya mata dokoki domin shirin auren ta. A lokacin da tsararrakin ta a wasu al’adun suke wasanninsu na yarinta, yarinya dai a wannan al’adar tana kulle a gida inda za a dinga ciyar da ita nama, kunun dawa da madara har sai tayi kiba. Yin kiba dai wata alamace ta kyau a yaren. Idan kuwa ta fara nono, iyayen ta zasu fada mata da ta guji duk abubu
Tab wan nan ai rashin addini ne kawai.
Allah Ya Kyauta, Gaskiya Mun Godewa Allah Daya Sanya Mu A Musulunci