ArewaRayuwaSoyayya
Abin da ake yayi

Soyayya bayan aure yafi dadi kuma shi yafi cimawa

Ba daga zarar anyi aure ake daina nuna soyayya ba, a'a soyayya bayan aure ita yakamata tafi

Soyayya bayan aure yafi dadi kuma shi yafi cimawa

Anyi wani taro na maza masu aure a garin KANO mai taken… “Yaya zaka zauna da iyalenka cikin farin ciki da annashuwa”…
Wanda Wata Kungiyar MATA suka hada domin daidaita dakuma sulhu tsakanin ma’aurata. Inda shugabar kungiyar HAJIA AMMI HAMZA TSAMIYAR ZUBAU ta bani Katin Gayyata. Mai gabatarda takarda farkon sai ya tambaya mahalarta taron cewa: “a cikin kunnan wanda yakeson matarsa yadaga hannu sama” duk sai suka daga hannunsu sama.

Sai yakara tambayarsu cewa:
“a cikin kunnan waye zai fada min lokacin daya budi baki yafadawa matarsa cewa yana sonta?”
Wassu sukace yau, wassu jiya. Wassu kuma ma bazasu iya tuna ranarba.

Sai ya fadawa mazajen kowa yadauki wayarsa ya rubuta ” I Love You Sweetheart ” ya turawa matarsa. Duk sai sukayi hakan. Sai kuma yabasu umurnin cewa su exchanging phones domin kowa yaga reply da’aka yiwa dan’uwansa.
Ganan amsoshinsun kamar haka:
1. Ka sake yiwa wata ciki kuma ko?
2. Da ne, amman ba yanzuba
3. Kanason nabaka bashin kudi kenan?
4. Me kayi kuma? Wannan karankam bazan yafe makaba
5. Menene wannan kenan?
6. Wata sabuwar wakace ?
7. Mafarki nakeyine ko gaskene ?
8. Idan baka gayamin wayece kayi niyan turawa wannan message din yau ka taro match …!!!
9. Kai ba! Nace maka kabar shaye shaye ka kiji !!!
10. Don Allah wayene wannan ?

Hmm! Mazan Nijeriya kenan. Idan ana soyayya ayita cewa I love you kamar yadda police ke loving N20, su wani I can’t do without you, su sweetheart I cares for u, su my life, my soul mate da sauransu. Amman daga sun samu sun dauke yar mutane shikenan, kamar masuncine da kifi a ruwa.

Yayinda yakeson kamashi zai sanyamar meat, amman daga yakamshi shikenan. Ko menene ke jawo hakan oho! Soyayya bayan aure itace wacce zakayita kasamu
lada a wajen Ubangiji.
A arewa, da zarar anyi aure angama cin amarci, sunanta da miji ke kunyar kira zai koma kira gatsau babu alkunya. Alllah Shi kyauta.

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: