Labarai

Babu wanda ya tsira’ a hadarin jirgin Ethiopian Airlines

Jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines Boeing 737 ya yi hadari a kan hanyarsa daga birnin Addis Ababa zuwa Nairobi

Jirgin saman kamfanin Ethiopian Airlines Boeing 737 ya yi hadari a kan hanyarsa daga birnin Addis Ababa zuwa Nairobi.
Jirgin yana dauke da fasinjoji 149 da ma’aikata takwas, kamar yadda kamfanin jirgin ya bayyana.

Fasinjoji 32 da ke cikin jirgin ‘yan kasar Kenya ne, sai 18 ‘yan Canada, da takwas ‘yan Amurka, sai kuma bakwai ‘yan Birtaniya.

Mai magana da yawun kamfanin ya ce hadarin ya faru ne da misalin karfe 08:44 na safe agogon can a ranar Lahadi, jim kadan bayan da ya tashi daga babban birnin kasar Ethiopia.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya ce za a fara aikin ceto, sai dai ya ce ba a san adadin mutanen da hadarin ya rutsa da su ba tukuna.

“Za a tura ma’aikatan kamfanin Ethiopian Airlines wurin da hadarin ya faru don su yi duk mai yiwuwa wajen aikin ceton gaggawa,” in ji kamfanin.

Firai ministan Ethiopia Abiy Ahmed ya bayyana sakon ta’aziyyarsa a shafinsa na Twitter ga iyalan mutanen da suka rasa ‘yan uwansu.

Wakilin BBCBBC Ji Tamirat daga sashen Amharic na BBC ya yi magana da wani mutum mai suna Bekele Gutema wanda yake wurin da hadarin ya faru.

“Fashewa da kara da gobara sun yi karfin da ba mu iya karasawa kusa da wurin ba. Komai ya kone kurumus. ‘Yan kwana-kwana da misalin karfe 11 kuma hadarin ya faru ne a karfe 8.”

Ya ci gaba da cewa “Na ga kimanin jirage masu saukar ungulu hudu a wurin yanzu. Babu wanda zai rayu daga hadarin,” in ji shi.

Kamfanin ya ce jirgin kirar Boeing 737-800 MAX, sabo ne kuma ba a dade da sayo sa ba. Har ila yau, ya ce irinsa ne wanda ya yi hadari a kamfanin Lion Air na kasar Indonesia a watan Oktoban bara.

Kamfanin jirgin yana galibin zirga-zirgarsa ne a nahiyar Afirka, kuma a shekarar 2010 wani jirgin kamfanin ya yi hadari a tekun Bahar Rum bayan da ya taso daga birnin Beirut, inda fasinjoji 90 suka rasa rayukansu.

Hakazalika a watan Nuwambar shekarar 1996 wani jirgin kamfanin ya yi hadari a kan hanyarsa ta zuwa Nairobi daga Addis Ababa, inda mutum 123 daga cikin fasinjojin jirgin 175 suka mutu.

Daga BBC Hausa.

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: