- MACE KO MATA.
Duniyar nan cike take da milyoyin MACE, amma kalilanne daga cikinsu suka can-canci lakabi da MATA.
Dan kawai ke mace ne, hakan bazai sa ki zama mata ba (ko da kuwa kina da aure).
Akwai wasu nagarta, da mace take samu, kafin ta zama mata ga mijinta.
Mafi akasarin maza suna yanke alaka, ko warware igiyar aure, idan suka fahimci macen da suke aure, bata can-canci zama mata ba.
Aure zai ba ki lakabin mata, amma mijinki ne zai tan-tance, ke mace ce ko mata.
Nagartar mace, wanda zai mayar da ita mata, ana samunsu daga ma’anonin kamalmar M. A. T. A.
M.= MAI HIKIMA…
Macen da za ta amsa suna mata, dole ta kasance mai hikima. Tunaninta ya kare akan yadda za ta tsara mijinta, ‘ya’yanta, gidanta da duk wani al’amuran da ya shafe iyalanta.
Za ta kasance mai ba wa mijinta, shawarwari masu nagarta, ta inda za su inganta iyalansu.
Cikin hikima, za ta tsara nan gaba. Baza ta damu da halin da take ciki a yanzu ba. Tunaninta yadda gobensu zai fi yau in su kyau.
Tunaninta ba a kan kudi, dukiya ko abunda mijinta ke samu bane, tunaninta akan yadda za ta inganta iyali ne..
A.= AIKI TUKURU…
Bata da cikin wadanda za su kasance cikin masu kasala.
Ba ta bukatar tsayuwa ko sa idon mijinta kafin tayi aikace-aikacen gida, irinsu. Wanki, wanke-wanke, shara, dafa abinci, tsabtace daki da gida. Da duk wani aikace-aikacen gida.
Za suyi aiki kafada da kafada da mijinta, wurin ganin sun ciyar da gidansu gaba. Za ta kasance tamkar mataimakiya na musamman a gare shi.
T.= TAUSAYI…
Mata, macece mai tausayi, tausasawa da nuna soyayya ga mijinta. Duk abinda ya sameshi, za ta ji tamkar ita ne ya sameta.
Alakarsu za ta kasance tamkar alakar zuciya da idanu. Idan zuciya ta kuntata, sai idanuwa su zubada hawaye. Za ta zama turke, shi kuma ya zama kamar igiya. Tausaya wa mijinta dayane daga cikin abinda zai mayar da ita MATA.
A.= AMANA…
Ta zamto mai rikon amanan mijinta. Murya. Dukiya. Gan-gan jikinta. Na mijinta ne shi, shi kadai.
Ba za ta ta6a cin amana ba.