LabaraiRayuwa

An Bi Ta Har Dakin Mijinta An Yi Mata Kisan Gilla A Jihar Kaduna

A cikin makon da ya gabata ne wasu wadanda ba a san ko su wane ne ba, suka kashe wannan baiwar Allah

Daga Bangis Yakawada

A cikin makon da ya gabata ne wasu wadanda ba a san ko su wane ne ba, suka kashe wannan baiwar Allah mai suna Aisha Sunusi, matar aure ’yar shekara 18, inda aka bi yo ta har cikin dakin mijin ta aka yi mata kisan gilla.

Lamarin ya auku ne a wata anguwa da ake kira Sabon Garin Bomo dake garin Bomo a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.

Wakiln mu ya binciki yadda lamarin ya faru, kamar yadda mijin marigayiyar ya shaida masa a yayin da ya ke gudanar da binciken kwakwaf kan lamarin.

Danjuma Mai Kayan Miya shine mijin matar da aka yi wa kisan gillar; ya ce, a ranar Juma’a da safe ne bayan ya fita zuwa kasuwa wajen da yake gudanar da sana’arsa ta sayar da kayan miya, sai matar tasa, Aisha, ta kira shi a waya cewa, ta na son ta sha garin rogo, sai yace, to zai sayo ma ta.

Danjuma ya ce, “kafin komawata na tsaya na yi aski, kafin na kai ma ta abinda ta bukata.” Ya cigaba da cewa, ya na Isa kofar gidan sai ya ga kofar a bude, ba kamar yadda ya saba bari ba.
Danjuma ya ce, ganin haka ne ya sa ya dan ji wani abu a zuciyarsa, amma sai yayi mata sallama, kamar yadda ya saba duk lokacin da ya dawo, amma ya ji shiru.

Ya ce, “Ina shiga falo, sai ban gan taba, amma sai naji tayi nishi mai karfin gaske a cikin uwar dakin mu.
Hakan ya sa nayi sauri na shiga cikin dakin.” Danjuma ya ce, yana shiga, sai ya ga matar tasa a kwance cikin jini, ga raunuka a kanta munana.
Hakan yasa shi fita da gudu, don neman gudunmawar jama’a. Nan take ya samo jama’a suka zo cikin gidan su ka ga matar rai a hannun Allah.
Hakan ya sa a kayi gaggawar kai ta asibiti, don ceto ranta. Bayan kai Aisha asibiti ne ba jimawa, sai rai ya yi halinsa.

Binciken da LEADERSHP A YAU ta gudanar ya nuna cewa, wadanda su ka aikata wannan ta’addancin sun yi abinsu ne da rana-tsaka misalin karfe 2-3 na rana, yayin da jama’ar unguwar kowa ya tafi masallaci sallar Juma’a.

Malam Yusuf Adam, wanda shi ne mai anguwar da lamarin ya faru, ya tabbatarwa da wakilinmu faruwar lamarin, kuma ya ce, “gaskiya ba muji dadin faruwar wannan lamari ba, don wacce aka kashe da mijinta muna zaune lafiya da su; babu wata matsala tsakani

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: