LabaraiRayuwa

Abokin Mijina Ya Sadu Dani Har Na Samu Ciki

Tsautsayi Yasa Abokin Mijina Ya Sadu Dani Har Na Samu Ciki, Taskar So Yanzu tashin hankalina shine me yakamata nayi na sanar da mijina?

Idan na fada masa hakan Zai iya zama sanadin mutuwar aurena Taskar SO Ko kuma nayi shiru? Idan nayi shiru kuma na cutar dashi da yawa

Kullum abokan mijina suna gidanmu kamar yadda shima yake zuwa gidajensu
Kamar masu wata ciyayya kullum da gidan Wanda zanje cin abinci, duk kuwa da mu matansu bama zumunci.

A cikinsu akwai wani da muna wasa dashi sosai musamman ma yafi kowa zuwa gidana Ni dai bansan ya akayi ma muka fara hira dashi sosai ba, har wasu lokutan zai shigo ko da abokin nasa baya nan ya zauna yaci abinci muyi ta hira

Anan na fahimci yafi mijina kirki sosai kuma yana da Saurin fahimta, don haka duk wata shawara sai na koma dashi nake yi duk wadda ta danganci zamana na aure kuma da taimakonsa ina samu mafita sosai.

Watarana yazo muna hira na zuba masa abinci yana ci muna hira, har zuwa lokacin da kowa yayi shiru ya rasa abin fada Bansan yaya akayi ba shaidan ya shiga tsakaninmu har muka aikata zina dashi ba

Muka shiga damuwa mu duka, tun daga ranar bai sake dawowa gidana ba Nima kuma naji bana son sake ganinsa Na zata komai ya wuce Ashe da sauran rina a kaba Kwatsam yanzu na fahimci Ina da juna biyu kuma bana mijina bane ba ne Damuwar yanzu bana son aurena ya mutu kuma nasan mijina da zafin rai, Indai yaji wannan labarin ba iya mutuwar aure bama wallahi har duka sai ya hada mun dashi. 

Dan Allah Taskar So strictly Hide My Identity Kuyi min post Domin wannan labarin da da hali ni a kankin kaina ma zan boyewa kaina, Shawara kawai nake nema, nayi Dana sani Mara Adadi wallahi ina son mijina bana son Rabuwa dashi
—————————————————————————————————————
Kuma Zaku iya Aiko Mana Da Labarinku Ta DM Mugun ji Mugun Gani Allah ya kiyaye mu

Labarai masu Alaƙa

Back to top button