Labarai
Abin da ake yayi

AREWA24 sunyi wani sabon shiri da zaifi Dadin Kowa

AREWA24 Tashan TV da tayi fice a duniya wanda take yada shirye-shiryenta a harcen hausa zalla

AREWA24 sunyi wani sabon shiri da zaifi Dadin Kowa

AREWA24 Tashan TV da tayi fice a duniya wanda take yada shirye-shiryenta a harcen hausa zalla kuma mai tsawon shekaru 4 da watanni da fara aiki a AREWAcin Nigeria ta sake shiri mai take Kwana Casa’in.

Shi wannan shiri ya tabo batutuwa da dama kamar harkan asibiti, Yan jarudu, Yan siyasa, Yan makaranta da Malamai, da kuma Yan sanda na kan hanya da sauran su,  Gidajen yada labari daban daban. Sai Malamai na addini, Yan daban siyasa.

Wannan shiri mai taken Kwana Casa’in jiya ne aka fara haska shi akan tashar AREWA24 wanda sun dauki tsawon lokaci suna tallansa da kuma aikinsa.

Kwana Casa’in yazo da karfinsa a inda mutani da dama sun nuna jin dadinsu a shafukan sada zumun ta na tashar AREWA24.  hakan yana nuna cewa shirin zai iya doke takwaransa mai suna Dadin Kowa wanda ya dauki kimanin shekaru 4 da watanni ake haskawa a tashar AREWA24.

Ya hada mutani da dama da kuma kwarewa akan aiki musamman jaruman shirin kamar su Falalu A Dorayi, Sani Mu’azu, Shehu Hassan Kano da babban Director na shirin kuma Director na Dadin Kowa wato Salisu T Balarabe, Saidai shirin yayi anfani da wasu jaruman shirin Dadin Kowa kamar su Ladingo maman su alawiyya, da kuma Samuel da sauransu.

Shirin zai ringa zuwane a duk sati ranar Lahadi da misalin karfe 8 na dare sabanin yanda shirin Dadin Kowa ke zuwa ranar Asabar karfe 8 na dare a kowani sati sau daya.

 

Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa

Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.

 

Labarai masu Alaƙa

Back to top button