LittattafaiShahara
Abin da ake yayi

Dan Babban Gida 01

Samrah Ya kamata ki canza kayan
Nan na jikin ki haka kike so mu fita cikin unguwar nan duk jama’a na kallon mu?
Sai da na gama zuge tee din jikina sannan na dube kausar wadda tun dazo idanun ta ke kai na, kallon tsaf nayi mata sanye take da wata duguwar brown din hijabi mai hannu.
Sai da naja wani dan guntun tsaki sannan na ce mata, meye haka kausar kin wani saka wata doguwar hijabi sai kace matar liman, kausar ta kalle ni tayi wani dan murmushi da bai kai ciki ba ta ce Eh!
matan liman din ce kuma wanan shigar ita ce duk wata musulmar kwarai zatayi don kare martabar ta, itace kuma Allah (SwT) Ya umarce mu da muyi, ba irin shigar ki ba irin ta jahilan fark…kee kausar!

Na dakatar da ita cike da tsiwa cikin daga murya nace What are you saying kausar?

Wa’azi kike min ko me? Sai da na matso kusa da fuskar ta sannan na sa dan yatsa na ina mai nuna ta, nace idan wa’azi zakiyi kije masallaci ina jin can za’a fi sauraron ki ba nan ba ina gama fadar haka na figi jakata nayi gaba.. ta biyu ni cikin sassarfa tana bani hakuri.

Samrah ,samrah! AMMI ce ta kwada min kira.

Sai da na Dan yi tsayowar minti biyar sannan na koma cikin gidan ina mai yatsinar baki, tsaya mata nayi aka ina taunar cingam.

Ammi ta ajiye tire din da ke hannun ta sannan ta dube ni, ina zaki ne samrah? Baki ga magrib ya kusa ba? Ko so kike baban ki ya dawo yayi ta fada ne? Meyasa ne ke kam bakiji samrah? Eyye!
Shiru nayi mata.

Na turo baki Ammi fa yanxu zan dawo plss na.. na tafi? Wani assignment ne fa aka bamu kuma gobe ne za’ayi submitting dole na gama shi yau.. cikin raina nace (astagfurullah) nayi ma Ammi karya.

Sorry Ammi!

Shigowar safwan kanina ne ya dauke ma Ammi hankali, Anan ne ni kuma na samu damar fita!

Ina fita na tarar kausar bata nan cikin raina nace ko a jikina! Na san gida ta koma abun ta, ita wai a dole uztaziya.

Mtsww wani dan kuntun tsaki na saki na ci gaba da tafiya ta ina wakar india.

Ina shirin tsayar da mai taxi kenan sai naga wata katuwar jeeb prado ta parker gaban neighborhood din mu ,wani saurayine kyakyawan gaske naga ni ya fito daga motar sanye yake da duguwar farar jallabiya irin ta larabawa.

Yana fitowa ya zuba man wani kallo wanda yake cike da tsana da kyama, kallon jikina nayi riga ce da lagins a jikina kuma ni dai ban ga abun kyama a tattare da niba,

Murguda masa baki nayi nace mutum sai kallon tsiya sai kace wani maye.

Na jiyo kenan zan shiga taxi kenan, a tsammani na shi din ba bahaushe bane saboda yanayin shi da naga ni irin na larabawan usul ne.

Hannun sa ya sa ya kamu riga ta, ya tsura min kyawawan blue eyes din sa, ya daka man tsawa What do you just say,? Ina jin haka ciki na ya fara motsi saboda tsabar tsoro cikin raina nace ashe dai yana jin hausa?

Ware masa nawa brown eyes din nayi cike da tsiwa nace how dare you touch me! Yayi saurin sakina ya daga murya yace Repeat what you just said to me.

Tsaki na ja masa .mtsww nace I can’t! Na shiga taxi cikin sauri ina mai kara kiran sa Maye kawai !

Cikin daga murya ina dariyar mugunta.

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: