AddiniIslamLabarai

Datti Assalafy ba Musulmi Bane -Inji Muneerat Abdussalam

Wata Sabuwa: Datti Assalafy ba Musulmi Bane -Inji Muneerat Abdussalam

A kwanakin baya fitaccen marubucin Hausa a yanar gizo kuma mai fafutukar kishin Addini da Al’adar Malam Bahaushe wato Datti Assalafy yayi wani rubutu na jan hankali ga wata fitacciya a shafukan sada zumunta na yanar gizo wato Muneerat Abdussalam bisa zarginta da yada barna a bayan kasa wadda ta saba da tarbiyya, addini dama al’adar Malam Bahaushe, an tafka muhawara masu a zafi akan wannan batu, sai dai ana tsaka da hakanne Muneerat ta sake karbar addinin musulunci a zagaye na biyu a babban masallacin kasa dake birnin tarayya Abuja.

Tun bayan wannan lokacin Muneerat ta cigaba da wallafa bayananta cikin Video cike da shiga irinta ta tarbiyyar Islama sai dai ta samu koma baya daga masu bibiyarta, ana tsaka da hakane kuma cikin daren jiya Asabar Muneerat ta fitar da wani sabon Video mai zafi wanda take martani ga Malam Dattin inda ta bayyana cewa ba musulmi bane kuma yana cutar da musulunci.

Acikin Videon dai ta yi kalamai masu munin gaske inda ta kalubalanci Datti kan ya je ya koyo aikin jarida inda ta bada misali da Ja’afar Ja’afar, ta kara da cewa wasu ba kiranta suce tazo gari kaza ta samesu inda suma ta zagesu tas da nasu rabon na zagi da ashariya.

Har izuwa yanzu dai Malam Datti Assalafiy bai wallafa komai a shafinsa dangane da wannan batu ba.

Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?

Labarai masu Alaƙa

Back to top button