RayuwaShahara

HALACCIN MAKOBTA 1 

A tsakiyar 2013 ne, adaidai lokacin da matsalar hare-haren boko haram ya yi kamarin da har ta kai ga an katse mana network na wayoyin sadarwa, al'amarin ya faru a wani dare da ba zan ta6a mantawa da shi ba.

HALACCIN MAKOBTA 1
(Jarumta ko sayar da rai?)
Adamu Maikudi

A tsakiyar 2013 ne, adaidai lokacin da matsalar hare-haren boko haram ya yi kamarin da har ta kai ga an katse mana network na wayoyin sadarwa, al’amarin ya faru a wani dare da ba zan ta6a mantawa da shi ba.

A wannan lokacin kusan duk wani rai da ke rayuwa a cikin kwaryan garin Damaturu da kewaye to yana cikin yanayi ne na rashin tabbas, idan gari ya waye to fa sai ka ga ka kai dare kamar yadda idan daren ya yi to babu tabbacin za a iya wayar gari da kai saboda yadda yaran boko haram su ka matsa da kashe mutanen gari ba-ji-ba-gani don an kai matsayin da an ma rasa waye su ke kashewa waye zai iya tsira?
A lokacin ne dare daya aka taba yanka sama da mutum goma a cikin unguwa guda, ba a maganar dauki daya daya da kullum sai an wayi gari da shi kamar kiran sallah.
Wannan shi ya sanya zullumi da karin tashin hankali a zukatan al’umma koyaushe mutum yana cikin fargaban za a iya far masa.

A irin wannan lokacin a wani dare ina bacci, zirga-zirgan Maman Ammi ya farkar da ni, da farko na dauka shigowa gidan aka yi to amma daga baya na fahimci ashe amai ne ya matsa mata haikan, hankalina ya yi mugun tashi saboda ganin yadda ta fara galabaita cikin kankanin lokaci.
Duk wani agajin gaggawa na yi kokarin bata amma aman sai ya ta’azzara. Wannan ya kara daga min hankali.

Wannan hali da ta ke ciki ya sa na fara sake-saken yadda zan yi na kai ta asibiti duk da halin da ake ciki na rashin tabbas. Tsakani na da asibiti tafiyar kafa ce da ba za ta wuce mintuna sha biyar ba to amma check point uku ne na hadakar Sojoji da ‘Yansanda zan ratsa wanda shi ne babban tashin hankalin.

Makocina Bayo na fara bugawa kofa cikin daren na yi masa bayanin halin da ake ciki sannan na gaya masa zan miko Ammi da Aman wanda a lokacin bai wuce wata shida ba a duniya su kwana a wajen su don ba zai yu na tafi na bar su su kadai a gida ba kowa.

Muna tsakiyar magana da shi ne sai Mokocinsa da su ke cikin gida daya Mal. Ahmed ya ji motsin mu ya fito shi ma.

Anan mu ka fara tattauna yadda ma za a yi na iya ratsa wadannan check points din har mu kai ga asibitin? Anan Mal. Ahmed ya ce idan dai za mu samu a bude mana check point din farko mu wuce to sauran masu sauki ne don haka shi zai fito da motarsa ya kai mu asibitin, jin haka sai ya kara min kwarin guiwa na ce su jira ni na je neman izini a check point din farko wadda shi ne mafi kusa da inda mu ke shi ne kuma na farko.

Na ratsa duhun daren na tunkarin wajen da check point din ya ke zuciyana cike da tarin fargaba da kuma tunanin me zai iya faruwa?

Tun kafin na kai kusa da su na fara ihun neman agaji don su jiyo ni kar su ganni haka bagatatan wani mai saurin hannu yq bude min wuta musamman da ya ke hade su ke da ‘yansanda bugu da kari dama unguwar ta mu ta yi kaurin suna saboda a nan aka fatattaki Abubakar Shekau.
“Help! Somebody help me!”
Haka na rika fada har na isa check point din babu wanda ya amsa min amma ina sane cewa lallai wasun su suna kallona tun farkon hawa na kan titin.

Ba zato ba tsammani hasken tocila mai karfin gaske ya dauke min idanu sannan wata tsawa ta biyo baya.
“Who are you?”
Ba a kashe tocin ba aka ci gaba da zubo min tambayoyi masu turerreniya da juna a rude na dinga amsa wanda na samu na ji daidai wanda ban ji ba na share na amsa na gaba.

A karshe su ka bar ni na karo cikin su, Dansanda daya da Soja daya kowanne dauke da bindiga su ka sani a tsakiya a lokacin da na ke yi musu bayanin halin da na ke ciki.
“Ga shi kuma ba mu da mota a nan kusa balle su kai ku asibiti” Sojan ya fada cike da tausayawa.
“Idan dai za ku bar mu mu wuce muna da mota”. Na fada da kwarin guiwa.
“What?” Dansandan ya fada cikin karaji kai ka dauka kunama ya taka.
“Cikin daren nan da private car?” Ya sake fada.
“Is dangerous”. Shi ma Sojan ya fada.
“Don kuna iya haduwa da ‘yan patrol su bude mu ku wuta!”
“Idan ma mun bar ku kun wuce nan bana tsammanin sauran check point din za su bar ku ku wuce”. Sojan ya sake fada.
“Idan dai za ku bar mu nan mu wuce sauran ma ba matsala Inshaaa Allah” Na fada.
“Okey” Sojan ya fada. “Bari na je na gayawa Oganmu mu ji me zai ce”. Ya nufi inda Ogansu ya ke kwana ya bar ni tare da Dansandan da ke ba ni shawarar indai na koma na ga jikin da sauki to mu hakura sai gari ya waye zai fi.

Lokacin da ya dawo ya ce Ogansu ya ce su bar mu mu wuce amma yana kara tabbatar min hatsarin da na ya ke gaban yana da yawa.

Na ce ba komai na yi musu godiya na koma bayan na gaya musu kalar motar duk da a cikin zuciyata ba ni da kwari guiwar zuwa asibitin a wannan lokacin.

To amma halin da na koma na same ta a ciki shi ya tabbatar zuwa asibitin babu makawa.

Labarai masu Alaƙa

Rubuta ra'ayi a kasa

Back to top button