RayuwaShahara

HALACCIN MAKOBTA 2

Lokacin da na koma ban 6oye komai ba game da yadda mu ka yi da Sojojin na gayawa su Mal. Ahmed bayan mun tsaya mun dan yi jugum kowa zuciyarsa tana magana da shi, ni ina tunanin wane hali ma zan koma na same ta a ciki? Kila ma ta gama galabaita ko ma ta mutu

2. Lokacin da na koma ban 6oye komai ba game da yadda mu ka yi da Sojojin na gayawa su Mal. Ahmed bayan mun tsaya mun dan yi jugum kowa zuciyarsa tana magana da shi, ni ina tunanin wane hali ma zan koma na same ta a ciki? Kila ma ta gama galabaita ko ma ta mutu!

Mal. Ahmed ne ya katse shirun ya ce min “Maza (haka ya ke kira na) ka je ka duba condition din da ta ke ciki yanzun kafin mu san me muke ciki”.
Cikin sauri na nufi kofar gidana zuciyata tana ta saka min ina warwarewa.

Halin da na koma na same ta ya fi wanda na bar ta a ciki tsanani da muni don ta baro cikin dakin amma ta fadi a kasa ta kasa tashi sama-sama numfashinta ya ke fita.
Na dauke ta na tallafi kanta akan cinyoyina kana na fara kiran sunanta.
“Ummi…” Sai da na kira ta sau uku sannan ta amsa da kyar a na ukun.
“Bara na dauko miki hijabi mu tafi asibiti”. Don na gama yanke shawara ko ni kadai ne zan kai ta asibitin ba zan bari ina kallo ‘yar mutane ta mutu a hannuna ba, tuni zuciyata ta gudurta min kara mu mutu a hanya tare da na zauna ina kallon ta har ta mutu.

Cikin kankanin lokaci na sanya mata hijabi kana na ciccibi Ammi da ta ke ta sharar baccinta na fito da ita na mikawa Bayo ita.
“Ka mika ta wajen Maman Sadiya (Matarsa)”.
Ya karbe ta tare da tambayar ina Aman din fa? Na ce masa zan dauko shi shima yanzu.

Fitowar da na yi da Aman motar Mal. Ahmed na tara a kofar gidana ashe yana ganin fitowa ta da Ammin ya fahimci zuwa asibiti babu fashi don haka ya shiga ya fito da motarsa.
Ya karbi Aman daga hannuna ya ce “Je ka fito da ita!”.

Na koma cikin gida na ciccibo Maman Ammi da kyar don Mashaa Allah ce. Na kwantar da ita a bayan motar a lokacin shi ma Bayo ya mika Ammi wajen Iyalinsa har ya fito da nufin karbar Aman amma sai na yi wani tunani.
“Za mu tafi da Aman”.
“Saboda me?” Su biyun duka suka bukata.
Na karbi Aman daga hannun Mal. Ahmad na rungume shi a kirjina. ” Duk checkpoint din da muka isa zan fito da shi a hannuna kafin na tunkare su, ganin yaro a hannuna zai hana su bude wuta”.
Duk su ka yarda da ni sannan mu ka shiga mota mu ka dauki hanya, bayan Bayo ya sa min wasu dunkulallun kudi a aljihu na.
“Yanayin nan da ake ciki ba a san yadda mutum ya ke ba ga wannan should be in case”.
Mu ka bar shi tsaye a kofar gida cikin jimami.

Mun fara samun turjiyar farko tun daga checkpoint din da na fara zuwa na sanar da su.

Kuskuren da aka yi shi ne, sun toshe hanyar da na yi amfani da ita lokacin da na zo wajen su da kafa ta yadda dama mota ba za ta iya wucewa ta wajen ba don haka sai mu ka bullo musu ta arewa maimakon ta kudu da su ke tsammanin mu bugu da kari jami’an tsaron da su ke 6angaren arewan sam ashe ba su san da zuwan mu ba kwatsam su ka hango motar mu ta tunkaro su gadan-gadan saukinsa ma mun kunna inner light.
Da kyar da sidin goshi su ka amince na samu suka bar ni na karasa in da su ke bayan na fito daga motar da Aman rungume a hannuna.
Su ka ce sam su ba su san da zuwan mu ba, babu wanda ya gaya musu, muna cikin haka aka yi sa’a daya daga cikin wadanda na samu da farko daga wancan daya bangaren ya sheko da gudu ya gaya musu lallai na zo dazu na gaya musu za mu je asibiti Ogansu yana sane, amma Sojannan ya ce sai ya ji daga bakin Ogan sa da kunnensa sannan za mu wuce, a karshe ya yarda zai je ya ji daga bakin Ogan don da farko ma cewa ya yi babu inda zai matsa sai dai mun ja motar mu mu koma.

Bayan ya ji da kunnensa sannan ya bude mana muka wuce.

Haka fa mu ka rika fama daga zuwa wannan checkpoint din zuwa wancan har Allah ya kare mu muka isa asibitin lafiya batare da ko korzanen jiki ba sai tsananin tsoro da fargaba. Don akwai checkpoint din da mu ka je suka ce ina bude kofar motar za su harbe ni, kawai mu koma koma mene ne sai da safe a haka na bude motar na fito ina sauraron saukar harsashi amma sai Allah ya sa ba su harba ba, daga baya Sojan ya tabbatar min ba don yaron da na fito da shi a hannuna ba to da sai dai uwata ta haifi wani. Na ce masa albarkacin haihuwa na fara ci tun daga yanzu shi ma Allah ya bashi dan da zai ci albarkacinsa.

Lokacin da mu ka isa cikin asibitin sai mu ka zama ababen kallo saboda mamakin yadda aka yi mu ka samu zuwa asibitin sannan su ka fara kokarin ceto rayuwarta cikin kankanin lokaci ta dawo cikin hayyacinta aka samu nasarar gano matsalar aka kuma magance ta nan take.

KARSHE!

Sai mun hadu a HALACCIN MAKOBTA kashi na biyu

Labarai masu Alaƙa

Rubuta ra'ayi a kasa

Back to top button