Adam A ZangoShaharaTaurarin ArewaWakoki

Ni ne Bahaushen da na fi kowa suna a duniya : Adam A Zango

A wani sakon video da Jarumi Adam A Zango ya fitar a shafin sa na Instagram yace Ni ne Bahaushen da na fi ko wane Bahaushe suna da masoya a duniya.

Ni ne bahaushen da na fi kowa suna a duniya.
A wani sakon video da Jarumi Adam A Zango ya fitar a shafin sa na Instagram yace Ni ne Bahaushen da na fi ko wane Bahaushe suna da masoya a duniya.
Yace ba shine ya fada hakan ba masu bincikene kuma masana su suka fada hakan. Yakuma karba sako daga wurin wani masoyinsa wanda ya tabbatar da hakan ina ya jero wasu hujjoji da dama, wanda duk ya nuna cewa jarumi Adam A Zango ya cika sunan sa na Jarumi.
Gasu Kamar Haka:

TABBAS GASKIYA NE ADAM A ZANGO YAFI KOWANNE BAHAUSHE SUNA A DUNIYA A DALILINA

1  Adam zango shikadai NE jaruminda yake fita wata kasar ba Nigeria ba yatara al’umma kamar yana kasarsa ta haihuwa..
2  Adam zango shikadai NE mawakin da yafi kowanne mawaki a arewa yawan tarin masu kallon waka, I Dan yasa wakar sa a shafin YouYube… karfa kuce iya hausawan arewa.. A a har wasu yaren GA MISALI ice prince zamani har yau wakarsa a YouTube me suna BOSS ba a kalleta kamar yadda aka kalli wakar Adam zango ta GAMBARA ba.. kuma abin mamaki anan shine itafa wakar gambara Shekararta daya da doriya da saki ita kuwa wakar BOSS anfi shekara uku dasakinta.

3 Adam zango shikadai NE jaruminda indan zai haska film a cinema ake cikar da babu wani jarumi ko jaruma da ya isa yatara al’umar dayake tarawa.. MISALI lokacin da zai haska film din GWASKA RETURN kowa yasani tunda film house cinema yake bai taba cika irin wannan ba.

4 Adam zango mawaki NE nasan wasu zasuce meyasa nace yafi wasu jaruman…MISALI ALI NUHU..shifa ba waka yakeba kuma babu wata kasa da Ali nuhu zai je ya nishadartar da mutane kamar yadda Adam yakeyi kaga bai cika jarumiba..saboda shi jarumi kullin so akeyi idan ya bayyana GA jama a to ya nishadan tar dasu ta yadda zasu ji dadin ganinsa..

5 RAHAMA DA ALI NUHU DA HADIZA GABON SUNFI Zango followers hakane Amma jama a kusani followers basu ne suke tabbatar mana da cikar stardom ba …MISALI kowa yasan AKON shine Wanda yafi kowanne mawaki suna da fice a yankin AFRICA..Amma abin mamaki WIZKID Yafishi followers…kaga kenan followers on Instagram bawani abu bane. Kuma fa kusani anayin cheat da followers dinnan.

6 Adam zango shikadai jarumin da duniya kannywood ta tasoshi agaba tasamasa ido duk abinda zaiyi suna kalle dashi kuma yafi kowanne jarumi makiya a kannywood..

7 Adam zango shikadai idan zaiyi aure Duniya take cece kuce akan aurensa Sai kace shikadai ne yataba aure a duniya.

8 Adam zango shikadai ne yafi kowanne jarumi fuskantar wariya ta fanni danne masa hakkinsa a matsayinsa na Wanda yafi wasu daukaka. Musamman idan akaga in ankirashi zai samu wani Abu Sai aki kiransa, Sai akira wadanda basu kaishi shahara ba..

 

Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa

Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.

Labarai masu Alaƙa

Duba Har ila yau
Close
Back to top button