Kalaman SoyayyaLabaraiSoyayya
Wasu Alamomin Da Zaki Iya Fahimtar Zaki Dace Da Miji
Zamantakewar aure ga ma'aurata
Ba kowace mace take dace wajen samun miji na kwarai ba. Hakan kuma yana faruwa ne tun a lokacin soyayya yan mata basu cika amfani da hankalin su wajen iya fahimtar ko wannan Saurayin da suke soyayya zai iya zama miji na kwarai idan kin aure shi.
Ga wasu alamomin da zaki iya ganowa idan wanda kike soyayya dashi zai iya zama miji na kwarai bayan auren ku:
1: Baya miki karya.
2: Yana ciki miki alkawari.
3 : Yana da kula da addini.
4: Baya shaye Shaye.
5: Bai da rowa.
6: Yana da zuciyar taimako.
7: Yana matukar mutuntaki.
8: Yana da lokacin ki.
9: Yana damuwa da damuwarki.
10: Baya kyamar mutane su kusance shi.
Muddin namijin da yanzu haka yake sonki da aure ya siffantu da wadannan É—abi’u yi maza kiyi wuf da shi.