Waye sarkin Kannywood Ali Nuhu ko Adam A Zango
Waye sarkin a masana'antar Kannywood dake Nigeria wannan shine babban abunda ya jawo cecekuce tsakanin jaruman guda biyu wato Ali da Adamu
Waye sarkin a masana’antar Kannywood dake Nigeria wannan shine babban abunda ya jawo cecekuce tsakanin jaruman guda biyu wato Ali da Adamu
Ali Nuhu shine akewa lakabi da King of Kannywood a labarai amma babu wani taro ko kuma biki da hadakan yan wasan kannywood sukayi na zaban sa Sarki, wannan sunan ya samune a kafafun sada zumun ta da sauran su. Shi kuma Adam A Zango ana masa lakabi da Prince wato yarima tun asalinsa , shin dukkanin su sun dace su zama jagora na Kannywood, kuma me yasa basu jituwa wato shiri tsakanin su, yaushene za’a samu sarkin Kannywood?. wannan sune batu da ke yawo a shafukan sada zumunta. A Yaune Adam A Zango ya saki wani faifayin video wanda wasu jarumai maza guda biyu suke kalaman batanci wanda shi Adam A Zango yanuna dashi akeyi. Kuma ya fada cewa Ali Nuhu shi yasa aka masa haka, ya kuma dau alwashin zai rama dan kuwa yana shirye tsaf duk wanda ya taba masa ahalinsa shima zai taba nasa, yace rubutu kawai ya yi bai fara fidda video ba, A lokacin da ya ya fara fidda sakon martani na video zai ga wanda zai fasa kuma yace Ali Nuhu yasan sa yasan kuma shi wayene.
Shin ko me yake kawo ire-iren wannan sabanin da Adam A Zango da Ali Nuhu ke fiskanta ako wani lokaci.
A satin da yagabata Jarumi Adam A Zango yace shine bahaushen da yafi kowa suna da farin jini a duniya. Ko wannan kalaman yasa Ali Nuhu yaji zafi ya mayar masa da martani ta wurin yaran gidan sa?.
Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa
Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.