Labarai
Abin da ake yayi

An Bayar Da Belin Wasu Daga Cikin Wadanda Ake Zargi Da Kashe Janar Alkali

Babbar kutun Jihar Pilato dake sauraron karar wadanda ake zargi da hannu kan kisan hafsan sojin nan, Manjo Janar Idris Alkali, ta bada belin mutane 21 daga cikin mutane 28 da aka gurfanar da su a gaban kotun.

Bayan sauraren bayanai daga lauyoyin masu shigar da kara da masu kare wadanda ake tuhumar, Alkalin kotun mai shari’a, Daniel Longji, ya bada belin mutane 21 kan Naira miliyan ‘daya kowannen su, da sanya hannun wadanda zasu tsaya musu, yayin da shugaban al’umma zai tantance wadanda zasu karbi belin.

Tun farko da ma’aikatar shari’a ta jihar Pilato ta karbe karar daga hannun ‘yan sanda.

A halin da ake ciki dai an sake mayar da wadanda aka bada belin nasu zuwa cikin kurkuku har sai an kamala cika sharudan da aka gindaya.

Alkalin kotun ya kuma dage sauraren karar zuwa ranar 25 ga wantan daya na shekar ta 2019.

  1. Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji daga VOA Hausa https://www.voahausa.com/a/an-bayar-da-belin-wasu-daga-cikin-wadanda-ake-zargi-da-kashe-janar-alkali/4705217.html

Labarai masu Alaƙa

Rubuta ra'ayi a kasa

Back to top button