ArewaNijeriya

Yadda yan Sara-suka Suka Sare Min Hannuwa, Inji Habibu

Ina zaune tare da aboki na cikin dare wurin karfe daya na dare, sai aka kira shi da waya, sai yace mun an kira shi da bakuwar lamba

Yadda yan Sara-suka Suka Sare Min Hannuwa, Inji Habibu Nakasari
“Ina zaune tare da aboki na cikin dare wurin karfe daya na dare, sai aka kira shi da waya, sai yace mun an kira shi da bakuwar lamba, sai ya tsallaka titi ya tsaya bakin wani kangon gida yayi waya sannan, bayan ya dawo sai yace min mahaifinshi yace ya tafi ya nemo mishi shayi (shayin buzaye), sai nace masa yanzu dare yayi ba’a samun shayi yanzu, sai yace zaije ya dubo, sai nace masa ka tafi da mashin dina sai yace a’a, daga nan sai na hau mashin dina na wuce gida shima ya hau nashi mashin ya wuce”.

“Ina tafiya gida sai na ajiye mashin dina bakin kofa na tafi in bude kofa domin in sanya mashin din, sai kawai naji ana buga mini katako, adduna, har jini ya rufe idanuna !! Ashe har sun cire mun Hannuwa ban sani ba, daga nan sai suka tafi da mashin dina hakan dai shine yadda yan sara-suka suka mun”. Inji Habibu

Allah ka tona asirin ko su waye suka yi wannan ta’addancin.

A kwana kin nan Kasar Nigeria tana fiskantar matsalan tsaro da kuma tashin hankali kamar karkuwa da mutani, fashi da makami da dai sauransu.

Wadannan rikice rikencen dai sun samu tushine game da albarkatun kasa da yankin Arewacin Nigeria ke dashi inji wani babban Malami a jihar Kano dake arewacin Nigeria.

Koshin wani mataki gwantin kasan ke kokarin dakile ire-iren wannan lamarin, a shekaran jiya dai gwannatin taraiyya ta dakatar da aiki da kuma duk wani abunda ya shafi ma’adanai a fadin jihar zamfara bayan nazari da tayi.

Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa

Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: