LittattafaiSoyayya

Dan Babban Gida 03 Labarin soyayya na yan zamani

Ina shiga kicin na tarar da Ammi tana wanke wanke. Nayi sauri na rufe mata ido Ammi ta taba hannu na tace samrah?

Dan Babban Gida 03

Ina shiga kicin na tarar da Ammi tana wanke wanke. Nayi sauri na rufe mata ido Ammi ta taba hannu na tace samrah?

Nayi sauri na cire hannu na ina dariya
Ammi yunwa nake ji na fada ina mai shan wani juice da ammi ta hada na kwakwa ina shanyewa nace Ammi tace dama dole kiji yunwa ai kin fita tunda safe ba ko breakfast 1 Ajiye cup din da ke hannu na nayi nace Ammi kin san mene?

Tace a’a sai kin fada nace hmmn
Dr .Arrogant ne ya hana mu fita lectures muke tayi kuma baya son late coming a class din shi. Ammi na yanka water melon tace shi kuma lecturer din ya sunan sa kenan Dr.arrogant? Dariya nayi nace Ammi sunan sa Dr. Ahmad zaid, Egyptian ne yana koya mana physics. Oh God! Kiran sunan sa ma yasa raina ya baci that arrogant jerk na fada ina mai tsaki mtsww Ammi na shirya drinks a try ta kalle ni samrah! Malamin ki kike zagi ko? Nayi dariya nace Ammi ya cika girman kai ne
Ammai tace toh naji, shiga dakina ki dauko man waya ta ki zo kici abinci
Ina mika ma Ammi wayan ta na bude freezer na dauka chocolate ice cream. Ina sha naji wani sanyi hmm yummy na fada.
Ammi wannan ma ya isa
Ammi na motsa miya face samrah ice cream din safwan ne bakin shanye naki bane jiya?
Na turo baki nace ammi yunwa fa nake ji
Ammi ta kada kai tace kida safwan ne ni dai ba ruwana , nace Ammi pls don’t tell him nice na sha tace toh.
Cikin sauri nayi huggin dinta nace thanks Ammi nayi mata peck a cheeks din ta Har zata fita nace Ammi na ga mai martaba dazo a parlor me ya kawo su?
Ammi na jin na fada haka tace nima ban sani ba, kije kiyi wanka kizo kiyi wanke wanke

Ammi, Ammi! Safwan ya shigo da sauri cikin kicin ina ganin sa na zaro ido OMG! This boy is back am finish na fada cikin raina
Nayi sauri na boye bayan dinning table. Ammi naga mai martaba sun zo yace ma zai bani doki nayi hawan sallah babba. Cewar safwan.
Ammi tayi murmushi tace Allah?

Safwan!

Safwan yace eh Ammi ai zamu je sallah katsina ko?

Ammi ta dafa kan safwan tace eh safwan ko dan kai ai zamuje yawan sallah fada.
Cikin jin dadi safwan yace yawa Ammi zaki fada wa Abba ko?

Ammi tace eh mana tana murmushi Safwan naji haka yayi hugging Ammi yace you are the best Ammi in the world Ammar ne kwance dakinsa yana sauraron Qur’ani suratul Rahama.

Amma zuciyar shi har yau nazarin yarinyar yake da ya hadu da ita kwanakin baya a estate da mai martaba sarki ya aike sa wajan uncle khalid

Gashi sun kuma haduwa da ita yau gidan uncle khalid Rintse idanon sa yayi yana mai tunanin Al’amarin ko dai yar gidan ce? Tambayar da yayi wa kan sa kenan
No! Ya ba kansa amsa, koda ban san yaran uncle khalid ba nasan suna da tarbiya. yana jin kiran sallah ya kashe karatun Qur’anin ya mike Why am i even thinking about that manner less girl Tsaki yaja mtsww yana mai tuna haduwar su da shigar da ke jikin ta.. Yayi tir da halaye irin na ta Ya shiga toilet.
************************************
Bayan na idar da sallah Asuba nayi azkar na dauko Qur’ani ina biya hadda ta, sai kawai naga an bude kofan daki na
Ya samrah!

Rufe ido na nayi ina girgirza kai na, ina idar da ayan na bude ido na, safwan na gani tsaye yana kallo na, ya samrah ina ice cream dina? Na tambayi Ammi tace bata san wa ya dauka ba.

Rufe Qur’ani na nayi, na kalli safwan wanda ya cika pam da fushi kamar zaiyi exploding yana jira na bashi amsa amsa

Safwan nace maka ban san wanda ya sha maka ice cream ba kazo early morning kana tambaya na, kama yi sallah kuwa?

Nayi mana ya samrah ina so nakai ice cream dina school ne.

Mikewa nayi nace kai ka sani , sai ji nayi safwan yace What ya na mai nuna roban ice cream da yatsan sa. Ya samrah! Ya zaro idanun sa na kalle sa menene? You drank my ice cream! Ya fada yana daga murya.

Labarai masu Alaƙa

Rubuta ra'ayi a kasa

Back to top button