Zafafan Hotunan Mako

Labarin soyayyar laila majnun na ainihi

Nasan kun dade kuna jin Labaran Soyayya Amma na Tabbata baku taba cin karo da irin wannan ba Waye majnun laila ?

Laila: 💔❤️👨‍❤️‍👨❣️LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN❣️ 👨‍❤️‍👨❤️💔
.
Nasan kun dade kuna jin Labaran Soyayya Amma na Tabbata baku taba cin karo da irin wannan ba Waye majnun lailah?
.Wani mutumne da aka yi a daular banu umaiyya abisa zancemafi inganci. Sunansa shine “Qais Bn Mulawwah” daga “kabilar Banu Amir”,
.
Qais balaraben kauyene, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna “LAILA BNT MAHDI IBN SA’D” Amfi sanin Laila da sunan “Laila Aamiriya”, tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balagha.
.
A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai “Qais” ya rude soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi.

Domin a wannan lokacin ne “Qais” ya Lura da irin kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa “Laila”, a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar “Qais”, a cikin wannan yanayi ne “Qais” ya shiga rera mata waqoqin soyayya kala- kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin “Laila” ya nemi da “Qais” ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna sai da Qais ya bayar da raquma hamsin a gidansu “Laila” a matsayin kudin aure.
.Ana haka sai ga wani mutum da ake kira “WIRD BN MUHAMMAD” wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin ‘ya’yayen masarautar “Banu Umaiyya”, katsahan yayi ido hudu da “Laila” a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabobinta.

Daga wannan rana Soyayyar “Laila” ta hana Wird ya yi bacci a wannan dare! Cikin yan kwanaki kadan Iyayen “Wird” suka sauka a gidan su “Laila” dan neman aurenta ga dansu “Wird”.
.
A wannan rana da Iyayan “Wird” suka je ga mahaifin “Laila” sai da suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda “Qais” ya bayar!
.
Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan haka ne Mahaifin “Laila” ya kira‘yarsa “Laila” cikin daki yanai mata hudunbar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita!
.
Babbar Magana! Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince da auren “Wird” ba!
.
Kwatsam sai aka wayi gari “Qais” ya ji gari ya dauka da kace nace din an yiwa masoyiyarsa “Laila” aure, da “Wird”.
.
Wanne irin hali “Qais” zai kasance a wannan ranar?
.Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da “Qais” a matsayin abokai na din-din-din!
.
Wake waken soyayya sune zancensa, bashi da abokin hira sai wakar da yake yiwa “laila” ga kadan daga irin abinda yake cewa:
.zuwa ga Allah nake kai kukan son “laila” kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa zuwa a Allah.
.
Mara yanda da kafasa ta karye gashi kuma dangi sun gujeshe “Lallai” rasa iyaye abune mai girman gaske.
.
Haka “Qais” da aka yiwa lakabi da “Majnunu lailah” yake bin kwararo kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gushe ba harse da akayi masa lakabi da “majnunu laila”.!
.
Duk da cewa itama Laila tana matukar son
“Qais” (majnun) amma kuma hakan baya hanata ta
wahalar dashi, a wasu lokutan ma harda yi masa
wulaqanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi
wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake
shi yasa majnun awani baiti yace:
.
“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a
makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar
dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina
sonta) shin hakan da take ba laifi bane?”
.
Sai Malamin ya fadawa “Qais” cewa: “Wallahi da
sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita
hadu da bala’i”.
.
Daga nan “Qais” yace, sai na kasa mallakar idona
sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiqa min
aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta
duk da yake a duniya dan kadanne samunta.
.
“Qais” ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan
hali har sai da ya samu tabin hankali.Domin ya
kasance idan yaga yara suna wasan kasa yakan
zauna tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina gida irin
wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waqa:
“abokaina kuzo kuga gidana nida laila”….!
.
A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka
baiwa mahaifin “Majnun” wato “Qais” shawara da ya
daukeshi ya kaishi ka’aba (dakin Allah) ya umarce
shi da ya roqi Allah ya cire masa son Laila!
.
Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je
dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama
tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila
.
Sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka
daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da
nake yiwa “Laila” ba.
.
Ataqaice haka “majnun” ya rayu cikin wannan yanayi
na abin tausayi!
Ita kuwa “Laila” tuni wanda ya aureta ya dauke daga
kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi.
.
Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi
abinka da ‘ya mace mai rauni sai da rashin ganin
“Qais” ya haddasa mata ciwon zuciya .
.
Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda
tsananin soyayyar “Qais Majnun”!
.
Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta
Allah ya karbi rayuwarta!
.
A lokacin da “Majnun” yaji labarin rasuwarta sai da
yaje har kasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka
binne ta, a makabartar da aka binne “laila” a daidai
gindin kabarinta ya tare.!
.
Bashi da aiki sai kuka da wakokin soyayya a
gareta.
.
Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi
(Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan qabarinta, ko da
aka zo akaduba sai aka tarar Allah ya yi masa
cikawa!
.
Haka fa Allah yake jarabtar wasu da soyayya

Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa

Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.

Ra'ayi daya

Rubuta ra'ayi a kasa

Back to top button