Son annabi yafi ibada: Na dau hanaya zuwa wurin aiki tare da abokin tafiyana kamar ance daga kanka sama, a dai-dai lokacin da nayi nuni da hanuna sai sai naji abokin tafiyana yace kaikai la ilaha illallah muka hada baki da cewa toh, ba dan komai ba sai dan ganin wannan mota dauke da wani kalmomi da ya saba da shari’a na cewa son Annabi yafi Ibada, ire-iren wadannan abubuwan su suke kawo mana musifu da tashin hankali acikin kasa.
Hakan ya sa naji ya dace yan uwa musani annabi sonsa ibada ne a wurin mu ba sai ka fada ba ko ka rubuta, kuma shi annabi ba’a mai ibada Allah akeyi wa, Annabi dan aikene kamar sauran annabawa kamar su annabi Isah, Yusuf, da sauran su.
A lokacin da ka rike son Annabi kadai baka yin Ibada kamar su Sallah, Azumi Zakka, Hajji to tabbas baka cika musulmi ba dan kuwa sune cika ciken musulunci guda biyar harda kalmar shahada na shiga addinin wato lā ʾilāha ʾillā-llāhu muḥammadun rasūlu-llāh.
Ina fatan Allah zai bamu damar gane gaskiya, da ikon aiki dasu kuma kar wani ya rudemu da wani fasaha ko kuma balagar iya magana dan ya juya mana tunani da wasu kalmomi,
Wannan sakone ga dukkanin yan uwa musulmai mungode, kuma banyi wannan rubutun dan cin zarafi ko kuma cin mutuncin wani ba sai don gujewa da kuma karin haske garemu matasa, Allah kara mana soyayyar annabi da kuma aiki da shi acikin ibadun mu, ya kuma bamu makoma mafi kyau wato Al’jannar fiddausi.
Taskar So shafi ne dan samun labarai, rubuce-rubuce na nishadi na hausa da turanci daban a fadin duniya musamman wadanda ya shafi matasa da soyyaya a rayuwa
Muna anfani da suna daya aduk inda muke kuma haka a kafafun sadarwa na zamani wato kamar su Facebook, Instagram, Twitter, YouTube sunan kuwa shine Taskar So.
You must log in to post a comment.