Kalaman SoyayyaLittattafaiShaharaSoyayya

Dan Babban Gida 2

Misalin karfe 8.00 na dare na dawo gida, pls dont be surprise, as you already know am a party girl! Cikin sanda na shigo gida hannu na rike da takalmana ina tsoro kar Ammi ta ganni.. har na zo bakin kofa kenan zan shiga sai dai naji muryar ABBA

kee samrah!

Ya fada cikin daga murya daga ina kike! Hey guys am just speechless dont know what to say to Abba!..

Ba day ke nike magana ba samrah kinyi shiru kin kyale ni ko, yi hakuri Alhaji!

A heard a voice 4rm behind. Omg who was this angel that save me from Abba!

Sai da ta tambaye ni kafin ta tafi.. wani Assignment din makaranta ne taje yi ko samrah?

Daga idanuna nayi sai naga Ammi ta tsura man ido.. kada kaina nayi alamar eh!

Sannan Abba yayi fada kar a sake barin yaran sa fita da magrib.. Ammi tayi saurin amsa masa. Yana tafiya ta juyo kaina tace samrah! Look at me, na kallo ta da idanuwana da suka canja kalla cikin minti biyu sun koma jajar don kuka, tace haka mukayi da ke? Ba sai da nace maki ki dawo gida kafin magrib?

Ta shi nayi cikin sauri nayi hugging Ammi, Am really sorry Ammi ba zan kara ba ban samu taxi da wuri bane shi yasa.. Ammi ta tashi ta ce kije ki ci abinci kafin Abban ku ya fito yayi maki fada.

Murmushi nayi cikin raina nace Abba sai fada but he still love us.. Ammi ce ta kalle ni tace me kuma kike wa murmushi samrah, saurin tashi nayi nace Ammi ina safwan ya dawo daga tahfiz din daran ne?

Ammi na shirin fita tace eh yana waje tare da Abban ku kiyi sauri ki fito..
Yau bayan na dawo daga makaranta misalin karfe hudu na yamma , duk na gaji saboda azumin da nike yi na ranan litinin.

Ina shiga gate din gidan mu naga wata bakar Jeep anyi parking din ta cikin raina nace yau baki aka yi kenan gidan.
Ina shiga cikin palo naji gamm nayi karo da mutum, wata kara na saki

Auuuchh!! Ammi kaina!

Sai a lokacin ya lura da akwai mutum a gaban sa tsaki ya jaa mtswww don’t you hav eyes!! Bakya gani ne ya fada cikin daga murya.. Oh.. This arrogant man again? Mtsww na ja tsaki cikin raina nace mutum kullun fuska a daure ba ko fara’a sai shegen girman kai day Jan ajin tsiya.
Get out of my way ya fada yana mai saka hannun sa cikin aljihun wando sa. Da sauri na matsa na shiga cikin gida, Abba na gani tare da mai martaba suna magana, cikin sauri na zo zan wuce samrah!

Abba ya kira ni
Baki iya gaisuwa bane? Ko baki ga baki bane a gidan? Cikin sauri na duka na gaisar da su ,samrah ce haka ta girma? Naji
Mai mai martaba ya fada.
Ni dai nayi sauri na shiga kicin ina kiran Ammi.

Labarai masu Alaƙa

Rubuta ra'ayi a kasa

Back to top button