Nijeriya

Breaking: PDP ta lashe zabe a Bauchi da da kuri’u 29,933

A Jiyane hukumar INEC ta ci gaba da tattara kuri'un kanan hukumomi 20 dake jihar bauchi

PDP ta lashe zabe a Bauchi na kujerar dan majalisar Tafawa balewa na taraiyya.

A Jiyane hukumar INEC ta ci gaba da tattara kuri’un kanan hukumomi 20 dake jihar bauchi, kuma ta sanar da cewan dan takarar jam’iyar PDP ne na adawa ya lashe zaben da da kuri’u 29,933 wanda shi kuma dan jam’iyar APC ya samu kuri’u 25,210 kachal wanda alkalin zaben ya sanar da cewan dan takar jam’iyar PDP shine yayi nasarar cin zaben duk da cewa zaben gwamnar an dakatar dashi sabida kiran da gwamnar mai ci a jam’iyar APC wato Bar. Muhammad Abubakar ya kai sammaci a babban kotun nigeria dake abuja zuwa ga shugaban INEC da kuma Jam’iyar Adawa ta PDP ba tare da cewa yayi duba zuwa kundin tsarin hukumar INEC da kuma zabe na Nigeria wanda babu wata kotu da zata iya dakatar da yin zabe ko kuma aikin zabe.

Amma duk da hakan hukumar INEC ta bi dokar kotun inda ta sanar da cigaba da karban zaben karamar hukumar Tafawa Balewa wanda kuwa bata sanar da zaben jiha ba ko ci gaba da zaben jihar sabida dan sammacin yashefe zaben jihane ba na zaben dan majalissar taraiyya ba.

Labarai masu Alaƙa

Back to top button
%d bloggers like this: